Connect with us

Labarai

Shugaban hukumar NDDC ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake bincikarsa

Published

on

Shugaban Hukumar Raya Yankin Niger Delta (NDDC) Daniel Pondei ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake tsaka da gabatar masa da tuhuma, kan almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da aikatawa.

A dai-dai lokacin da Daniel Pondei yake bayar da bayani ga ‘mambobin kwamitin majalisar wakilan Najeriya ranar Litinin kan Niger Delta game da yadda hukumar NDDC ta kashe biliyoyin Naira, ya yanke jiki ya fadi.

Shugaban hukumar NDDC ya kasa numfashi inda ya kame nan take a kan kujerar da yake. Daga bisani ne kuma aka fitar da shi daga dakin taron.

Hakan ta sanya shugaban kwamitin majalisar wakilan da ke lura da yankin Niger Delta ya bayar da sanarwar tafiya hutun minti 30.

Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban hukumar NDDC Mista Pondei ya fice daga zauren binciken ba tare da an gama ba, inda ya zargi shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Tunji-Ojo da aikata rashawa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne, shugaban majalisar wakilan  Femi Gbajabiamila da shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Doguwa suka shiga sahun mambobin kwamitin domin cigaba da zama.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending