Connect with us

Labarai

Sama da naira biliyan 20 ‘yan fansho ke bin gwamnatin Kano – Hukuma

Published

on

Hukumar fansho ta jihar Kano, ta ce sama da naira biliyan ashirin ‘yan fansho suke bin gwamnati a jihar, yayinda aka bullo da wani shirin tantance su a fadin jihar.

A farkon makon nan ne, gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin tantance ‘yan fansho tun daga matakin kananan hukumomi zuwa jiha, domin magance wasu matsaloli da suka dabaibaye Hukumar fansho.

A ranar 14 ga watan Oktoban 2020 ne, gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi rahoton adadin bashin da ‘yan fanshon ke bin gwamnati.

Sani Dawaki Gabasawa, shine shugaban Hukumar, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Dala FM.

Saurari wannan bayani a kasa;

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!