Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Saudiyya ta kama mutumin da ya shigar da Dan Jaridar da aka yi masa iyaka

Published

on

An kama wani wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da wani dan jarida ba musulmi ba, Gil Tamari cikin birnin Makkah mai tsarki, wanda ya sabawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba.

Jami’an Saudiyya sun ba da sanarwar a ranar Juma’a cewa, dan jaridar Isra’ila Gil Tamari, wanda ya je Saudiyya, domin ba da labarin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai a can, ya yi amfani da damar kasancewarsa a masarautar, ya shiga cikin Makkah, ya zagaya, ya nadi wani bangare na tashar Channel 13.

Yada shirye-shiryen ya haifar da rudani da kuma gargadin cewa, zai iya lalata wani yanayi da ake gani tsakanin Saudiyya da Isra’ila.

Saudi Arabia, mahaifar Islama, ba ta amince da Isra’ila ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Makkah ya ce, an kama wani dan kasar Saudiyya tare da mika shi ga masu gabatar da kara.

Saudiyya ta dawo da maniyatan Kano 7 sakamakon samun su da takardar izinin shiga na bogi

Huduba: Mu nemi ilimi ko a ina ya ke – Limamin Madina

“Shi (dan kasar) ya yi jigilar dan jaridar da ba musulmi ba, wanda ke da shaidar zama dan kasar Amurka, zuwa cikin babban birnin Makka ta hanyar da aka tanada ga musulmi, wanda ya saba wa ka’ida.

“Duk masu shigowa cikin masarautar dole ne su mutunta kuma su bi ka’idoji, musamman wadanda suka shafi wurare masu tsarki.

“Duk wani cin zarafi za a dauki shi a matsayin laifin da ba za a amince da shi ba,” in ji jami’in ‘yan sandan.

Jami’in ya ce, an kuma aika da karar dan jaridar wanda ya aikata laifin zuwa gaban kotu.

Kakakin ya ce, an ga Tamari a cikin wani yada shirye-shirye yana tuki a kusa da babban masallacin Makkah tare da yin watsi da alamun titin da aka yi wa wadanda ba musulmi ba.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending