Connect with us

Labarai

Atiku ya buƙaci Birtaniya ta kawo ɗauki a kan tsaro da tattalin arziki

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tsokaci kan kara hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Birtaniya da Najeriya, wajen lalubo hanyoyin da za a magance matsalolin daza su amfani kasashen biyu.

Sanarwar da mai taimaka masa a kan kafafen yaɗa labarai, Abdulrasheed Shehu ya rabawa manema labarai, ya rawaito cewa, Atiku, ya bayar da shawarar ne a lokacin da tawagar babbar hukumar Burtaniya karkashin jagorancin High Catriona Laing ta gana da Atiku a gidansa da ke Abuja a jiya.

A yayin ganawar Atiku da bakinsa sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi tsaro, ilimi, noma, tattalin arziki da kuma samar da hadin kan kasa a Najeriya.

Babban Kwamishinan ya bayyana cewa, ganawar da tsohon mataimakin shugaban kasar wani bangare ne na ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnatin Burtaniya, domin inganta dimokuradiyya da sahihin zabe a Najeriya.

Da yake mayar da martani, Atiku ya nuna jin dadinsa ga tawagar da suka ba da lokacin gudanar da taron, ya kuma bayyana cewa, “dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya na da tarihi mai dimbin yawa, kuma yana da muhimmanci kasashen biyu su yi amfani da wannan damar wajen inganta al’amuran da suka shafi kasashen biyu tare da damuwa da juna.”

Wazirin Adamawa ya jaddada cewa, yana sa ran kasar Ingila za ta taka rawar gani wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyya a Najeriya, kuma yana da yakinin cewa, zaben shugaban kasa a 2023 zai kasance cikin gaskiya da adalci.

A kan batun rashin tsaro, ya yi tir da halin da ake ciki a kasar, ya kuma nemi taimakon Birtaniya musamman a fannin horarwa da musayar bayanan sirri.

Da yake magana game da tattalin arziki, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, idan aka ba shi dama ya jagoranci al’amuran Najeriya, zai tare da sauran abubuwa, zai kawar da tsarin musayar kudade da yawa tare da rage haraji don karfafa masana’antu na gaske da kuma bunkasa jari na gaske. Ya kuma yi alkawarin bunkasa harkar noma, domin samar da ayyukan yi ga al’ummar kasar nan.

Bugu da kari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana damuwarsa kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi da kuma rikicin da ke faruwa a fannin ilimi.

Ya yi alkawarin aiwatar da gyare-gyare a fannin ilimi, gami da sake farfado da shirin ba da lamuni na kudi ga daliban Najeriya. 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending