Connect with us

Siyasa

Mun yi kyakkyawar shirin marawa Atiku baya – Ƙungiyar Mambobin PDP

Published

on

Kungiyar mambobin Jam’iyyar PDP daga yankin Kudu maso Kudu da aka yiwa lakabi da kungiyar yakin neman zabe ta KARADE-MAZABU karkashin jagorancin, Ada Fredrick Okwori, ta ce Atiku ya na da ƙwarewar da zai iya jagoranci Najeriya.

Da yake magana a yayin ganawar ta su da suka kai wa Atiku ziyara a gidansa na Abuja, daya daga cikin ayarin, Honorabil Omoge Tamuno, ya ce, kungiyar tasu ta na da yakinin cewar tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya kubatar da ƙasar daga halin da ta ke ciki sannan ya sake dora ta kan tafarkin zaman lafiya da haɗin Kai, yana mai cewar Atiku yana cikin mutanen da suka farfado da tattalin arzikin kasar nan a baya.

Sanarwar da mai taimakawa Atiku Abubakar a harkokin yaɗa labarai, Abdulrasheed Shehu ya fitar ya ce, mambobin ayarin sun kada kuri’ar goyon baya ga dan takarar shugaban kasar na PDP a zaben na 2023, inda ya ce, sun yi kyakkyawan shiri domin samarwa Atiku Abubakar cikakken goyan baya daga tushe.

A nasa bangaaren, dan takarar shugabancin na Najeriya ya yi marhabin da bakin, kuma ya gode musu bisa ziyarar, inda ya bukace su da jajircewa wajen aiki, domin nasarar Jam’iyyar PDP a zaben badi don kyakkyawar makoma ga Najeriya.

Hangen Dala

Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Published

on

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.

Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.



Continue Reading

Hangen Dala

Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Published

on

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.

 

Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

 

Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.

 

Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.

 

A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.



Continue Reading

Hangen Dala

Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Published

on

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.

 

Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.

 

“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.

 

“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.

 

Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.

 

A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.



Continue Reading

Trending