Siyasa
Mutanen Jada ku sauke nauyin da ke wuyan ku – Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi kira ga mutanen yankinsa, da su sauke nauyin dake kan su na yin zabe, domin bashi damar karbar kasar don inganta makomar kowa.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a mahaifarsa ta Jada, yayin wata ziyara ta musamman da ya kai jihar Adamawa.
Ya jaddada aniyar sa ta kasancewa Jakada na gari ga mutanen sa da kasar baki daya inda ya yi alkawarin aiki domin dawo da zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban kasa idan aka zabe shi.
A cewar sanarwar, Abdulrasheed Shehu, mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai, ya ce, gwamnan jihar ta Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, godewa Atiku ya yi, saboda shigowa cikin al’umar sa. Inda ya bawa dan takarar ta PDP tabbacin cewar, za su yi aiki domin nasarar sa a zaben, domin bashi damar amfani da kwarewar sa da kishin sa wajen ceto Najeriya.
Da yake masa maraba, shugaban karamar hukumar Jada, Honorable Salisu Muhammed Solo, ya ce, suna mutukar alfahari da kasancewar Atiku dansu, inda ya yi alkawarin mara masa baya a zaɓen 2023.
A jawabin sa yayin taron, Sanata Dino Melaye ya bayyana muhimmancin ziyayar zuwa gida, inda ya ce, wannan ya nuna cewar, Atiku ya san asalin sa ba kamar wasu yan takarar ba wadanda suke cike da rudani game da asalinsu.

Hangen Dala
Yau shugaban kasa zai dawo daga Faransa

Bayan ziyarar aiki ta kusan mako biyu Zuwa kasar Faransa a yau litinin ake saka ran shugaban kasa zai dawo gida Nigeria.
Cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce kowa ne lokaci daga yanzu shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu zai sauka a Nigeria domin cigaban da harkokin mulkin kasar.
Hangen Dala
Kofar APC a bude take ga masu shiga – Abdullahi Abbas

Jamiyyar APC a Jihar Kano tace Kofar ta a bude take ga dukkanin masu son shigowa jamiyyar.
Shugaban jamiyyar na Kano Hon Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Abbas yace labarin dake yawo cewa akwai wadanda ke Shirin shigowa jamiyyar, su sani Kofar APCn a bude take tare da maraba ga dukkanin wadanda zasu shigo.
Koda dai Abdullahi Abbas yace shigowa APC ba zai hana tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, koma kaucewa hukumar EFCC da ICPC.
A baya bayan nan ne dai aka rinka yada cewa mabiya jamiyyar NNPP kwankwasiyya na Shirin shiga jamiyyar APC tare da madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Hangen Dala
Gwamnoni sun bukaci a kawo karshen matasalar Filato

Ƙungiyar Gwamnonin kasar nan (NGF) ta buƙaci jagororin jihar Plateau su haɗa kan al’ummar jihar mai yawan al’adu da ƙabilu domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu a jihar.
Shugaban ƙungiyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kwara – Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje.
“Muna kira da jagorori da masu faɗa a ji a duka garuruwan jihar da sauran fannoni da su haɗa hannu da gwamnan jihar wajen haɗa kan al’ummar jihar tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa”, in ji shugaban ƙungiyar ta NGF.
“Ya kamata shugabannin matasan al’umomin jihar su fito su haɗa kai wajen yin Allah wadai da tashin hankalin da ake samu a jihar, muna kira da a riƙa sasanta duka matsalolin da suka taso ta hanyar tattaunawa da lalama tare da girmama juna,” a cewar Abdulrahman Abdulrazaq.
Fiye da mutum 100 ne aka kashe cikin mako biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari a wasu garuruwan ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
A ranar Talata ne babban sifeton ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya ziyarci jihar inda ya sha alwashin kamo waɗanda suka ƙaddamar da kashe-kashen, da ya bayyana da na rashin imani, domin hukunta su.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su