Connect with us

Siyasa

Abubuwa biyar da za su magance matsalolin Najeriya – Atiku

Published

on

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bada shawarar kafa gwamnatin hadin kan kasa, domin tunkarar da kuma magance matsalolin da suke addabar kasar nan.

Da yake jawabin sa, a kan maudu’in Mika Mulki a Najeriya cikin karni na 21 a taron kungiyar Lauyoyi ta kasa NBA karo na 62 wanda ya wakana a jihar Legas, wanda babban lauya Olisa Agbakoba ya jagoranta.

Atiku ya ce, tabarbarewar al’amura a Najeriya da kuma alkaluman bayanai marasa dadi kan kasar, tun daga matsalar rarrabuwar kawuna da rashin tsaro da rashin aikin yi da fatara da sauran su, inda ya ce, abu mafi muhimmanci shi ne yadda za a magance wadanan matsalolin.

Ya ce, tarihi zai so mu hada hannu mu yi aiki tare, domin ceto Najeriya, kuma damar yin hakan ta sake samuwa yanzu. Ya ce, halin tabarbarewar da Najeriya ta tsinci kanta yanzu ya na bukatar mutum mai kwarewa ya karbi kasar, domin kubutar da ita daga durkushewa.

Ya kuma fadi bangarori biyar dake bukatar kulawa da suka hada da haɗin kan kasa da tsaro da tattalin arziki da rarraba Iko tsakanin turakun gwamnati da kuma ilimi.

Ya jaddada cewar, hadin kan kasa zai samu ne ta hanyar tafiya tare da dukkan sassan kasar nan ta hanyar samar da gwamnatin hadin kan kasa da sake fasalin kasar, domin kara karfin Iko ga shiyoyi, sannan kananan hukumomi zasu rage dogara da gwamnatin tsakiya. In ji Abdulrasheed Shehu
mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai da ya aikewa Dala FM.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending