Connect with us

Siyasa

A shirye na ke na yi aiki da abokan tafiya ta – Atiku

Published

on

Wasu ’yan takarar shugabancin kasar nan da suka fafata a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da ya gabata, sun yi alkawarin goyon bayan takarar Atiku Abubakar.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Atiku kan harkokin  yada labarai, Abdurasheed Shehu ya fitar, ya ce, tsofaffin ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jagorancin Mohammed Hayatudeen, sun yi wa Atiku biyayya a lokacin da suka kai masa ziyara. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Kalu Chikwendu, Tarry Oliver, Dele Momodu da Charles Ugwu.

Hayatudeen ya bayyana cewa, sun zo ne domin taya mai rike da tutar jam’iyyarsu murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani da kuma yi masa fatan alheri a zabe mai zuwa, tare da fatan Atiku ya samu nasarar lashe zaben.

Cif Dele Momodu ya bayyana mahimmancin samun dukkanin masu neman shugabancin kasar nan, wanda a cewarsa hakan zai tabbatar da samun nasara ga jam’iyyar a rumfunan zabe.

A cikin kalamansa ya ce, “Dole ne dukkan masu son tsayawa takara su hadu wuri guda don ganin jam’iyyar ta kai ga nasara, kuma na yi imanin cewa PDP na da mafi kyawun damar lashe zaben shugaban kasa a 2023”.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki su shiga tsakani, ya kuma yi kira ga kowa da kowa da su marawa jam’iyyar baya domin samun nasara.

Ya yi nuni da cewa, “kowane korafe-korafe a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, yana da kyau kowa ya taru; don haka hadin kan jam’iyyar zai haifar da nasarar zabe ga kowa da kowa.”

Mace daya tilo da ta tsaya takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da ya gabata, Mrs Tarry Oliver, a takaice nata jawabin, ta bayyana cewa, a matsayinsu na ‘yan takara na farko, suna tuntubar dukkan takwarorinsu tare da fatan kowa ya hau kujerar naki domin isar da jam’iyyar a dukkan zabukan. .

Ta bayyana tsayuwarta cewa, tsarin jam’iyyar zai karfafa tsarin hadin gwiwa wanda zai hada da shigar mata da matasa wanda zai baiwa jam’iyyar damar mayar da hankali kan yakin neman zabe.

A cewarta, jam’iyyar PDP iyali daya ce mai hadin kai, ta kuma baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa duk wani abu da ke faruwa a cikin jam’iyyar na cikin gida ne wanda a karshe za a warware shi cikin ruwan sanyi.

A nasa martanin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana jin dadinsa da ziyarar taya murna da suka kai masa tare da yaba musu bisa yadda suka amince da sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Atiku ya ba su tabbacin cewa, a shirye yake ya yi aiki da su a matsayin abokan tarayya, ta hanyar tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.

Ya kuma jaddada muhimmancin yin aiki tare a matsayin hadin kai a fafutukar ganin an ceto Najeriya daga mummunan shugabanci.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa aikin kwato kasar ba aikin mutum daya ba ne, hakki ne na hadin gwiwa.

Atiku ya bayyana cewa yayin da lokacin yakin neman zabe ke kara gabatowa, ya sa ran za a kara tattaunawa da kungiyar.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Labarai

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ƙaryata ficewar sa daga APC zuwa SDP

Published

on

Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya musanta wata jita-jita da ake yaɗawa kan cewar ya fice daga cikin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa, zuwa SDP, al’amarin da ya ce bashi da tushe ballantana makama.

A cikin wata sanarwar da mashawarci na musamman ga tsohon Sanatan a kafafen yaɗa labarai Ezrel Tabiowo, ya fitar a jiya Lahadi, ta ce jita-jitar da ake yaɗawa na cewar Ahmad Lawan ya fice daga jam’iyyar ta APC, ƙarya ce tsagwaronta.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar, sanarwar ta kuma ce, har yanzu Ahmad Lawan ɗan Jam’iyyar APC ne, kuma yana biyayya ga jam’iyyar, wadda yake alfahari da ita.

Continue Reading

Trending