Connect with us

Siyasa

PDP ta tsayar da ayyukan ta mako guda saboda mutuwar dan mawaki Davido

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun, ta dakatar da ayyukanta na tsawon mako guda, bayan David Adeleke, dan gidan zababben gwamnan jihar, Ademola Adeleke, ya rasa dansa mai suna Ifeanyi.

Shugaban riko na jam’iyyar PDP na jihar Osun, Adekunle Akindele, a cikin sakon ta’aziyya ga iyalan Adeleke a ranar Talata, ya bayyana rasuwar Ifeanyi, dan Davido da Chioma a matsayin wani lamari mai matukar bakin ciki.

Ya kuma umurci dukkan sassan jam’iyyar da kwamitoci da su dakatar da ayyukan domin nuna ta’aziyya ga iyalin Davido.

“Ta’aziyyarmu tana zuwa ga Davido, jakadan matasanmu. Muna mika ta’aziyya ga mahaifinmu, Dr. Deji Adeleke da dukan dangin Adeleke. Muna addu’ar Ubangiji Allah ya ba ‘yan uwa ikon jure wannan rashi maras misaltuwa,” A sanarwar.

Labari ya fito da sanyin safiyar Talata, 1 ga Nuwamba, 2022, na mutuwar Ifeanyi mai shekaru uku.

An tattaro cewa ya nutse ne a wani wurin ninkaya da ke gidan mahaifinsa na tsibirin Banana a Legas, wanda a yanzu haka ‘yan sanda sun tattara dukannin ma’aikatan gidan na sa, domin amsa tambayoyi.

Hangen Dala

Maja:- NNPP ta amince da tayin Atiku

Published

on

Jam’iyyar NNPP ta yi maraba da kiran da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi na dunkulewar manyan jam’iyyun adawa don kwato mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.

 

NNPP ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Kawu Ali, ya yi ranar Talata a Abuja.

 

Ali ya ce, “A kwanakin baya ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga manyan jam’iyyun adawa da su hade kai a matsayin hanyar da za a bi wajen ganin an dakile mulkin kama-kamarya da jam’iyyar APC mai mulki ke yi da kuma wanzar da Dimokuradiyya a kasar.

 

“Jam’iyyar NNPP tana ganin wannan kira na Alhaji Atiku Abubakar a matsayin kishin kasa kuma abin farin ciki ne wanda hakan yasa muke ganin wannan a wani mataki mai amfanarwa,” inji wani bangare daga cikin sanarwar.

Continue Reading

Hangen Dala

Gwamnatin Kano ta ja hankalin al’umma Kan hukuncin da kotun daukaka Kara za ta yanke

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu gabanin hukuncin kotun daukaka kara da za a yanke a gobe Juma’a.

 

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, ta hannun Sani Abba Yola, Daraktan ayyuka na musamman na ma’aikatar.

 

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar su guji tada tarzoma ko kalaman da za su tada hankali kafin da kuma bayan hukuncin kotun.

 

Dantiye, wanda ke mayar da martani kan hukuncin zaben gwamna da za a yi gobe da kotun daukaka kara a Abuja, ya jaddada bukatar jama’a su wanzar da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.

 

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen ganin an tabbatar da doka da oda don tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Continue Reading

Hangen Dala

Kotun daukaka Kara ta ayyana zaben kujerar Gwamnan zamfara a matsayin Wanda Bai kammala ba

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar Zamfara, a matsayin wanda bai kammala ba.

 

A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari’a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaben Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris din 2023.

 

Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.

 

Ta ce kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Zamfara, ba ta yi la’akari da hujjojin da masu ƙara suka gabatar ba – wato jam’iyyar APC .

 

Kotun ta kuma yi watsi da sakamakon da jam’iyyar APC da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC suka bayar na ƙaramar hukumar Maradun.

 

Don haka ta umarci hukumar zabe (INEC) ta gudanar da sabon zabe a ƙananan hukumomin uku, inda ba a gudanar da zabe ba a baya, ko kuma ba a ƙidaya sakamakon wasu tashoshin zabe ba.

 

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben watan Maris, Bello Matawalle ne sake kalubalantar hukuncin da karamar kotun zaben jihar Zamfara ta yanke, wanda ta kori shari’arsa bisa hujjar cewa ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji.

 

Tsohon gwamnan na Zamfara, wanda a yanzu yake rike da mukamin karamin ministan tsaro, yana neman wa’adin mulki na biyu ne bayan karewar mulkinsa na tsawon shekara hudu.

Continue Reading

Trending