Connect with us

Manyan Labarai

Corona Virus: Liman ya ja hankali a kan cutar

Published

on

Limamain masallacin ma’aiki dake garin Madinatul’munauwara, Abdul- bril bn Aiwan Affabiti ya ja hankalin al’ummar duniya da su zamo masu komawa ga Allah kan dukkanin al’amuran su ta yadda za a samu saukin bullar annobar cututtuka, irin su Corona Virus da take sarke numfashi, wanda yanzu haka take addabar al’ummar duniya musamman a kasar Sin wato china.

Limamain ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar sallar juma’a wanda ya gabatar yau a masallacin na ma’aiki dake garin Madina.

Da yake fassara hudubar ta yau jim kadan bayan kammalata, Malam Aminu Kidir idris wanda shi ne limamin masallacin Usman Bn Affan dake unguwar Kuntau a karamar hukumar Gwale ta bakin limamin ya ce,” Baya ga daukan matakan kariya da masana lafiya suke bayyanawa, a yawaita addu’o’I, zikirai da istigifari sune za su taimaka wajen shawo kan matsalar”. A cewar limamin ta fasarar sa.

Fassarar wani bangare kenan na hudubar msallacin ma’aiki dake garin Madinatul’munauwara, wanda limamin na yau Abdul- Baril Bn Aiwan Affabiti, wanda limamain masallacin Usman Bn Affan dake unguwar Kuntau a karamar hukumar Gwale a jihar Kano, Malam Aminu Kidir Idris ya fassara.

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!