Connect with us

Labarai

sakin baki ta Facebook a kan Ganduje ya jawa wani zuwa kurkuku

Published

on

Kotun majistret mai lamba 10 karkashin mai shari’a, Muhammad Jibrin, ta aike da wani mutum gidan gyaran hali.

Mutumin mai suna, Sadi Bala Lamido, a na zargin shi da laifin sakin baki a kan gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Kunshin zargin ya bayyana cewar, Sadi Bala Lamido, ya yi rubutu a dandalin sada zumunta na Facebook, inda ya yi wasu kalamai marasa kan gado, wadanda wasu ke zargin cewa da gwamnan Kano ya ke.

Yayin da a ka karanta masa tuhumar, mutumin Sadi Bala Lamido, ya musanta zargin wanda lauyan da ya ke kare shi ya roki kotun da ta sanya shi a hannun beli.

A nan ne lauyan gwamnati, Barrister Lamido Soron Dinki, ya ce ya na da suka kuma ya roki kotun da ta sanya wata ranar, domin ya yi suka a kan rokon bayar da belin.

wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewa, kotun ta tsayar da ranar 15 ga wannan watan, domin lauya Lamido ya gabatar da suka a kan rokon neman beli.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending